Me Yasa Kwamfutata Take Nauyi? Dalilai 5 Da Hanyoyin Magance Su
Me Yasa Kwamfutata Take Nauyi? Dalilai 5 Da Hanyoyin Magance Su
Shin ka taɓa kasancewa cikin gaggawa, amma da zarar ka kunna kwamfutarka sai ta fara "loading" taki budewa? Ko kuma kana tsaka da rubuta wani muhimmin aiki, sai kawai mouse ɗinka ya daina motsi? Wannan abun takaici ne sosai.
A wannan zamanin na fasaha, kwamfuta ita ce babban makaminmu na aiki, karatu, da nishaɗi. Idan tana yin nauyi (slow), hakan yana rage mana kuzari da productivity. A cikin wannan post, zamu duba dalilai 5 da suke sa kwamfutarka yin nauyi da kuma matakan da zaka ɗauka yanzu don dawo da gudun ta kamar sabuwa.
1. Shirye-shiryen Da Suke Tashi Kai-tsaye (Startup Programs)
Daya daga cikin manyan dalilan da suke sa kwamfuta daukar lokaci kafin ta bude shine yawan apps ɗin da suke ƙoƙarin buɗewa a lokaci ɗaya da zaran ka kunna ta.
Matsalar: Apps kamar Spotify, Skype, OneDrive, ko wasu tools na kwamfuta suna saita kansu su tashi "automatically". Wannan yana cinye karfin RAM da Processor kafin ma ka fara komai.
Maganin: Je zuwa Task Manager (Ctrl + Shift + Esc), danna bangaren Startup, sannan ka yi "Disable" ga duk wani app da baka bukata ya Bude da kansa.
2. Karancin Sararin Ma'aji (Low Disk Space)
Kwamfutarka tana buƙatar aƙalla 10% zuwa 15% na sararin samaniya (free space) a cikin hard drive ɗinka don ta gudanar da wasu ayyuka na cikin gida (temporary files).
Matsalar: Idan Hard Drive ɗinka ya cika (ya koma ja), kwamfutar ba zata sami wurin yin "virtual memory" ba.
Maganin: Goge bidiyo da hotunan da baka bukata.
Yi amfani da Disk Cleanup ko Storage Sense a Windows don goge tsofaffin files.
Yi la'akari da amfani da Cloud Storage kamar Google Drive ko OneDrive.
3. Kwayoyin Cutar Kwamfuta (Malware da Viruses)
Wani lokacin, nauyin kwamfutarka ba matsalar hardware ba ce, illa dai akwai wasu baƙi da ba a gayyata ba a cikinta.
Matsalar: Viruses da Malware suna gudanar da ayyuka a ɓoye (background process), suna satar bayanai ko tura sako, wanda hakan yana cinye dukkan saurin computer.
Maganin: Sanya ingantaccen Antivirus (kamar Windows Defender, Avast, ko Kaspersky) sannan ka riƙa yin "Full Scan" a kalla sau ɗaya a mako.
Shin yaushe ne rabon da ka yi "Update" na Windows ɗinka ko MacOS?
Matsalar: Kamfanoni suna fitar da update ne domin gyara kura-kurai (bugs) da kuma inganta saurin kwamfuta. Idan kana amfani da tsohon version, kwamfutarka zata riƙa fuskantar matsala da sabbin apps.
Maganin: Je zuwa Settings > Update & Security > Windows Update sannan ka danna "Check for updates". Haka nan, ka tabbata drivers na Graphics da Processor duk suna kan gaba.
5. Matsalar Hardware (Musamman RAM da HDD).
Wani lokacin kwamfutar ce ta tsufa ko kuma kayayyakin cikinta ba zasu iya ɗaukar nauyin ayyukan da kake yi ba.
Matsalar: Idan kana amfani da 4GB RAM amma kana son yin video editing ko bude shafukan Chrome guda 50, kwamfutar zata yi nauyi. Haka kuma, tsofaffin Hard Drives (HDD) sun fi sabbin (SSD) hankali.
Maganin: * Upgrade to SSD: Wannan shine canjin da zai fi ba ka mamaki. Sauya HDD zuwa SSD yana sa kwamfuta sauri kusan sau 10.
Ƙara RAM: Idan kana aiki mai nauyi, tabbata kana da akalla 8GB zuwa 16GB na RAM.


Post a Comment
0Comments