Alakar Yan Qur’aniyyun da Wahhabiyya: Tarihi, Akida, da Bambanci a Addinin Musulunci
Abd-Wahhab suna ne kamar Abd-Malik, Wahabiyanci darika ce kamar Malikiyya. Muhammad Ibn Abd al-Wahhab an haife shi 1703 ya mutu 1792 a karni na 18.
Ahlussuna suna kafa hujja da shi saboda nacewarsa a aiki da Qur’ani da hadisai ingantattu. Dan Saudia ne, kuma nan aka haifi Manzon Allah (s.a.w).
Izala kungiya ce, a karkashinta ana yin da’awa, da’awarsu tayi kama da irin da’awar Abd-Wahhab; riko da Qur’ani da ingantattun hadisai.
Amma Qur’aniyyun suna kin hadisai, yayin da Wahhabiyya ke hada su waje daya da Qur’ani dan fahimtar addini.
Don haka, Qur’aniyyun da Wahhabiyya ba su da alaka. Amma BH da ISIS suna da alaka da Wahhabiyawa tun da sun yarda da Qur’ani da hadisai.
Sai dai shi addini ba alaka bane, aiki ne da gaskiyar wahayi. Kungiyoyin ta’addanci da sunan Musulunci suna amsa Kawarijawa ne. Wannan ya sa Sheikh Ja’afar, Albani Zaria, da Sheikh Idriss Dutsen Tanshi suka yaki BH.
Zaman Dangungu tsohon dan Izala daga karshe ya koma kala-kato kamar zaman Dr. Bashir da Daurawa ne a Shi’a/braza tare da Zakzaky daga karshe su koma Izala/Salafiyya. Sahabbai yawanci ba musulmai bane kafin da’awar Musulunci.
Ba komai ke kunshe cikin wannan rubutun ba sai abin da malaman falsafa ke cewa “straw man fallacy”, ka kai suka wajen da ka ke kyama tare da lankwashewa kar a feso tiyagas ka shaka.


Post a Comment
0Comments