DRISHYAM 2 (ƊAN MANYA 2) – Fim ɗin da ya sake rikita masu kallo
Na daɗe ban ga fim ɗin da marubutan labari suka goge haddar masu kallo irin wannan ba. DRISHYAM (ƊAN MANYA) ya kasance ɗaya daga cikin finafinan da suka nuna zurfin hikima, dabaru, da kaifin tunani a fagen shirya labari.
Lokacin da kamfanin Algaita Dubstudio suka fitar da sanarwar sakin fassarar Ɗan Manya kashi na biyu, na yi mamaki ƙwarai. Na ɗauka an gama kashe zaren labarin tun a fim ɗin farko, musamman ganin irin yanda aka fafata tsakanin jami’an ‘yan sanda da Ajay Devgan (Vijay).
Tarihin Labarin Fim ɗin Ɗan Manya
A fim ɗin farko, an nuna irin ƙoƙarin da hukumomin ‘yan sanda suka yi wajen neman hujjar hukunta Vijay, wanda aka zarga da aikata babban laifi. Amma duk da haka, Vijay ya rike kansa da hikima, wayo da dabara, tare da goyon bayan iyalinsa — matarsa da ‘ya’yansa biyu.
Ko da bincike ya zame musu wahala, suka tsaya tsayin daka akan amsa ɗaya da suka haɗa kai a kai. Har ƙaramar yarinyar da ke cikin iyalin ta nuna jajircewa wajen kare sirrin iyayenta. Wannan ya nuna irin tsayin daka, haɗin kai da tsoron Allah a cikin iyali.
Sabon Bincike Bayan Shekaru Bakwai
Bayan shekaru bakwai, aka kawo sabon jami’in ‘yan sanda wanda ya buɗe kundin binciken tsohon laifin da ake zargin Vijay da iyalinsa da shi. Wannan sabon binciken ya sake ɗauko zaren labarin da aka ɗauka ya ƙare.
Abin da ya fi kayatarwa shi ne yadda marubutan suka haɗa sabon salo da tsohon labarin cikin natsuwa da basira. A tunanin mutane da dama, an riga an gama da lamarin, amma sai aka dawo da shi cikin sabon salo da ya fi na farko armashi.
Dabarun Vijay da Hikimarsa
A tsawon shekaru bakwai, Vijay bai taɓa sakankancewa ba. Ya san binciken na iya komawa kowanne lokaci, don haka yake rayuwa cikin tsarin shiri da tanadi.
Ya shiga harkar finafinai, ya buɗe gidan kallo, kuma ya rubuta littafi da ke ɗauke da labari mai kama da nasu. Duk wannan, a zahiri kamar kasuwanci ne, amma a asali, wani tushe ne na kariya da dabara don tabbatar da cewa komai ya kasance cikin tsari idan aka sake taso da binciken.
Har ma da CCTV Cameras da yake da su, sun kasance suna kallon ofishin ‘yan sanda domin bibiyar duk wani motsi da zai iya zama barazana gare shi. Wannan ya nuna irin kaifin basira da tsare-tsaren nesa da Vijay ke da su.
Ƙarshe Mai Cike da Mamaki
Daga ƙarshe, Vijay ya sake waske wa jami’an ‘yan sanda da kotu. Ko da bayan sabon bincike, ba a iya samun wata hujja guda ɗaya da za ta tabbatar da laifinsa ba.
Wannan ya caji hankalin kowa, musamman sabon jami’in da aka kawo wanda aka san shi da basira da ƙwarewa. Duk da haka, jahilin da ake rainawa ya gagari wannan jami’i mai ilimi. Wannan ne ya sanya wannan fim ɗin ya zama abin koyi da tunani mai zurfi.
Darussan Rayuwa Daga Fim ɗin Ɗan Manya 2
1. Ka shirya domin kowace irin faɗuwa
A rayuwa, duk inda kake hangen nasara, ka kuma kalli yiwuwar faɗuwa. Ka tanadi magani tun kafin matsala ta bayyana.
2. Ka kare sirrinka
Sirrinka na iya zama maɓallin nasararka ko hanyarka ta lalacewa. Mutane da yawa suna samun hanyar cutar da kai ne ta sanin wani sirri daga gare ka.
A fim ɗin nan, sirrin da matar Vijay ta faɗa wa maƙociya ne ya zama hanyar da suka sake dawo da bincike.
3. Ka zama jajirtacce
Jajircewa da tsayin daka sune mabuɗan nasara. Duk wanda yake son rufin asiri da nasara a rayuwa, dole ya kasance mai ƙarfin hali da haƙuri.
4. Kada ka raina baiwar kowa
Baiwa tana zuwa daga Allah, ba ta dogon karatu ba. Wani da ake raina shi, na iya zama wanda zai hana ka sukuni. Hikima da basira ba sai da digiri ake samunta ba.
DRISHYAM 2 (ƊAN MANYA 2) ba kawai fim ne da ke nishadantarwa ba, amma darasi ne game da rayuwa, dabaru, sirri da ilimi.
Ya tabbatar mana cewa hankali da shiri sun fi ƙarfin iko da kuɗi a lokuta da dama.
Fim ɗin ya dace da masu son finafinan bincike, tunani, da dabaru, kuma fassarar Algaita Dubstudio ta sake tabbatar da cewa Hausa tana da manyan masu fassara da ke iya kawo labari cikin daɗin ji da inganci.
Ƙarshe
Idan har baka kalli ƊAN MANYA 2 ba tukuna, ka tabbatar ka kalla. Fim ne da zai ƙara maka ilimi, natsuwa, da tunani mai zurfi.


Post a Comment
0Comments