Yau Shekaru 14 Da Kisan Shugaban Kasar Libya Muammar Gaddafi

Nuhu Saad Kumurya
By -
0
Yau Shekaru 14 Da Kisan Shugaban Kasar Libya Muammar Gaddafi



 Yau Shekaru 14 Da Kisan Shugaban Kasar Libya Muammar Gaddafi 


A ranar 20 ga watan Oktoba 2011 sojojin ‘yan tawaye 'suka kama shugaba Muammar Gaddafi na Libya da dansa Mutassim a garinsa na Sirte,  jim kadan bayan kamun su ka kashe shi.


Mutuwarsa ta zo ne a karshen yakin basasar Libya a shekara ta 2011, wanda ya kawo karshen mulkinsa na shekaru 42. 


An kama Gaddafi ne ya yi yunkurin tserewa daga Sirte a cikin ayari a lokacin da birnin ya fada hannun 'yan adawa. Wani harin da NATO ta kai wa ayarin motocinsa, ya tilastawa Gaddafi da masu tsaronsa neman mafaka a wani babban bututun magudanar ruwa. Mayakan ’yan tawayen majalisar rikon kwarya ta kasa (NTC) ne suka gano shi.


Hotuna daga wayoyin hannu (smartphone) sun dauki hotuna yayin da aka kama Gaddafi yana zubar da jini, an yi masa duka, da kuma cin zarafinsa. Rahotanni masu cin karo da juna sun bayyana dangane da ainihin musabbabin mutuwarsa, amma duka sun rawaito an kashe shi jim kadan da kama shi.


Tun da farko dai jami'an kungiyar yan tawaye ta NTC sun ce an kashe Gaddafi ne a wata arangama da aka yi da su, amma wasu shaidu sun ce "wanda suka kamashi ne suka harbe shi". Binciken likitoci daga baya ya tabbatar da mutuwarsa sakamakon harbin bindiga da aka yi masa a kai da kuma cikinsa.


An baje kolin gawar Gaddafi ga jama'a a wani wuri mai sanyi da aka ajiye gawar a birnin Misrata' kafin a binne shi a asirce a wani kabari da ba a sani ba, a ranar 25 ga watan Oktoban 2011. An boye wurin da aka binne shi don hana shi zama wurin ziyara ga magoya bayansa. 


ALLAH YA ISA


YA ALLAH YA JIKAN MUAMMAR GADDAFI DA RAHAMARSA AMEN 🙏




Post a Comment

0Comments

Post a Comment (0)